Posts

Showing posts with the label from Imrana 08107324541

KYAWAWAN NASIHOHI 42 GA DAN'UWANA MUSULMI.

Image
1. Idan za ka nemi aure , ka nemi mace mai addini, kada ka biye wa kyau, dukiya. Haƙiƙa kyawu da dukiya za su ƙare, amma idan ka auri mai addini za ka yi rayuwa mai daɗi da ita, kuma abar birgewa ga mai kallo. 2. Ina gargaɗin ka a kan auren kyakkyawar mace wace ta fito daga mummunan gida. 3. Duniya jin daɗi ce, mafi alherin jin daɗinta mace ta gari. Wannan ya sa idan Allah ya ba wa mutum mace ta gari ya yi bankwana da rigima, damuwa, ƙunci da yawan mantuwa , domin kuwa idan mutum ya auri mace ƴar bala'i za ta rikitar da shi ta riƙa sanya shi yin ƙabali da ba'adi a cikin sallarsa. Kuma koda yaushe zai kasance cikin tunani da jin tsoron abin da zai biyo baya a duk lokacin da ya shiga gidansa. 4. Kada ka kula yarinyar mutane inba aurar ta za ka yi ba. Ka ji tsoron Allah ka daina hure wa ƴaƴan mutane kunne kana aikata alfasha da su. Shin za ka so a yi wa ƴarka ko wata ƴar uwarka irin abin da kake yi wa ƴaƴan wasu na rashin ɗa'a, ko dai ƴaƴanka da ƴan uwanka sun fi n...