sarkakiyar soyayya part 3
![Image](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEhxWhyphenhyphenBUIdwSOirGEvMamv7gl8ax09JAfaFT0MJMiYUVRGladUeKKv5DQH3WSsUmM1YclVlAsY2fsjnQ7OqPU-4rbkGTIwqGAsEh_9RP3CXJ462Ru44xTeX_ig3f8iWG3ZKNZxY8KLNw82v/s1600/1652002347849915-0.png)
…… INA ASHE GUDUN BANZA NAYI HAR GIDA ZATA BIYONI TAMIN. Cikin sauri na juya da gudu nabar cikin garejin ko kayana ban chanja ba. Ina fita ko mashin dina ban dauka ba gudun karna tsaya dauka tazo tasa meni. Ina fita bakin titin dayake garejin namu a bakin hanya yake. Cikin sauri na tari me adaidaita sahu nace yakaini wani unguwa dake kusa da unguwarmu. Ana saukeni a unguwar na rasa inda zanje kawai sainayi shawaran inkoma gida na bugawa wani dan garejin mu waya nace yatawo min da mashin dina gida yace to. Haryake gayamin cewa ameera tasha kuka acikin garejin waina yaudareta. Sauri nayi na kashe wayan na fada cikin wani botiq nasayi kaya domin cewa yanda akemin kallon babban yaro a unguwar mu bazan iya shiga da kayan gareji ba. Bayan nasiyi kaya na chanja saina bugawa abokin harkata usman na gayamai cewa yaufa rana ta kwa6e. Kazo da motarka ka daukeni kasan bazan iya hawa adaidaita sahu inzo gidaba dan kasan ana biki akan layinmu akwai yan mata dayawa yace to. Minti 20 yayi ...