sarkakiyar soyayya part 4
……
Nan take ameera tace to kaban labarin naka naji. Nace to. Nan take nafara bata labarin kaman haka.
Harabar hotel din cike yake da jama’a makil. Kowa ka kagani acikin hotel din cike yake da farinciki gamida annashuwa. Bakomai akeyi ba a harabar hotel dinba illa partyn bikin babban abokin mu BANGIS MC.
N hussaini na guys komai akeyi mune agaba saboda muna manyan abokan ango.
Gaskiya partyn ya hadu domin cewa a ranar na bawa idona hakinsa. Sbd naga rawan manyan yan mata da manyan yara. Ana cikin tsakiyar party sai naji dj yana cewa ana neman HUSSAINI NA GUYS DA AMEENA a filin rawa. Cikin sauri na juya domin naga wacece ameena. A gaskiya kallo 1 nayi mata naji gabana yana faduwa. Harnayi niyan bazan jeba amma muna hada ido da ango bangis mc yayimin wani kallo. Kawai saina fito filin rawa domin cewa inde ban fito ba bazaiji dadi ba. Ina fitowa fili dj yace ayanzu N.guys da Ameena zasuyi mana rawa domin su taya ango da amarya
murna. Dj yana gama maganar sa akasa mana wakar [mallet ft wizkid] wakan da idan naje clup shi ake sakamin. Amma a yanzu gaba daya sainaji gabobin jikina sunyi nauyi dakar nake iya juyasu. Nan take muka fara rawa sai fili ya dauki ihu da
sowa kowa sai shigowa fili yake yana ciki.
Muna gaba rawan na koma wajen zaman na zauna. Amma saide naji zuciyata ta kamu da
tsananin kaunar ameena.
Ina daga kaina saina hangi ameena ta nupi inda ake aje motoci tana waya cikin sauri na tashi na nupi inda take. Ina zuwa nace da ita AMINCIN ALLAH YA TABBATA GA KAMALALLIYAR MACE MA’ABOCIYAR KARAMCI DA SANIN YA KAMATA.
Kafin ta amsamin maganata saida tamin wani murmushi
tace dani GAISUWA DA FATAN ALHERI YA TABBATA GA MA’ABOCIN DADIN BAKI DA SANIN YA KAMATA. Nace nagode sarauniyar yan mata nazo makine da wani sako me matukar tauri da nauyi a cikin harshe wanda kawai furta makine zaisa nasamu kwanciyar hankali da nutsuwa
acikin zuciyata. Ameena tace dani fadi abinda yake tafe dakai
koda yakai nauyin dutsen dalane zan iya dauka.
Nace da’ita nasan cewa ke daban kike acikin yan mata.
Dukdade cewa yau nafara ganinki amma na fahimci cewa baki da girmankai ga hakuri da
sanin yakamata shiyasa nakeso ki duba ki agazawa rayuwata.
KO ZAN’IYA SAMUN WAJE ACIKIN ZUCIYARKI??
Hmmm tayi murmushi tace dani sainayi tunani kaban number ka anjima zan kiraka na baka amsa nace to cikin sauri na gaya mata number na kaman haka 08093217xxx ina gama bata tamin wani murmushi tace saikaji kirana.
Ina bata number handset dina tamin murmushi ta juya ta koma inda ake party saida nakai kusan minti 5 awajen kafin nima na koma wajen party. Anyi party lafiya anraka ango gidan amaryar sa. Tun lokacin da muka dawo gida misalin karfe 10 na dare nake jira naji wayan ameena domin
nasan matsayin danake ciki.
Har karfe 11pm ameena bata bugomin waya ba nan take hankalina ya tashi har nake tunani cewa karde ta manta dani shiga dakina nayi na kwanta akan gado da niyar nayi bacci amma ina bacci ya kaurace daga idanuwa na. Ji nayi handset dina ya dauki kara alamun anturo sako. Cikin sauri na bude sakon naga anyi rubutu kaman haka DAFATAN KADAWO GIDA LAFIYA RABIN RAINA ZUCIYATA RUHINA KAINA GABA DAYA NA MALLAKAMA KAINE FARKON SAURAYI WANDA YAFARA KWANTAMIN ACIKIN ZUCIYATA. INA SONKA hussaini ina gama karanta wasikan nayi ihu nayi tsalle tsabagen murna kamin nima na mata replay da SARAUNIYAR ZUCIYATA A RAYUWATA BAN TABAYIN FARIN CIKI BA IRIN NAYAU DAKIKA AMINCE DA SOYAYYATA BA’ABINDA ZANCE ILLAH ALLAH YA CIKA MANA BURIN MU.
Saina tura mata sakon
Soyayyar mu da ameena tayi nisa banayin sati sainaje gidansu waya kan alalace zamuyi sau 20 arana.
Wata rana ranan lahadi da misalin karfe 4 na yamma nakai ziyara gidansu rabin raina ameena. Bayan ta budemin falon saukan baki na gidansu
tacemin bara taje gida cikin gida ta dawo. Tana tafiya sainaji alamun shigowan mota cikin
gidan [ashe babanta ne yadawo alhaji sulaiman] alhaji sulaiman yana fita daga cikin motansu saina nufo cikin gida yana zuwa daidai bakin kofan falon saukan baki saina gamshi na gaisheshi amma ya amsa aciki ciki yace dani kaine kake zuwa gun yata amina? Nace masa eh?
Yacemin waye babanka?
Wani makami babanka ya taba rikewa a 9ja sanata ko dan majalisa gidajen sa nawa??
Hmmm nan take naji kirjina yana dukakan uku,
Zamuci gaba a part 5 gobe in Allah ya kai mu.
Very nice
ReplyDelete