Posts

Showing posts from July, 2022

TSAMMANIN DAKE ZUCIYOYIN MUTANE GAME DA JIMA'I A ZAMANIN YAU.

Image
TSAMMANIN DAKE ZUCIYOYIN MUTANE GAME DA JIMA'I A ZAMANIN YAU  ●••••○•••••●•••••○•••••●•••••○•••••●•••• Rubutawa Dr. Ibrahim Y. Yusuf Bayani ne mai nauyin gaske da kuma ke kunshe da dunqulallun bayanai masu mahimmanci. kamar yadda na alkawarta abaya zanyi!  Toh saide da farko zan fara da cewa; gaskiya idan kasan ko kinsan bakya iya tsayawa ku karanta dogon post a natse komi mahimmancinsa toh ina rokonka dakai gaba kurum, domin post din me tsayi ne kwarai, ahakan ma na takaita shine bakuma nason rabashi saboda hakan zai iya sa wani parts din ya zamo missing... saika karancesa zaka fahimcesa da kyau....  Amma nayi BOLD HEADLINES da paragraph aciki da zaka iya fahimtar inda ka tsaya koda baka karancesa lokaci daya ba. 🌻🌻🌻 Hakika rayuwa da kuma zamani sun canza takai ga wasu abubuwan da ada ake lullu6esu ayau sun fito fili har sunfara zamowa bakomi ba. Da yawa mutane basu dauki tattaunawa game da irin wadannan ke6antattun al'amura na jima'i wani abu ba musamman ...

TARIHIN TAFAWABALEWA KASHI NA DAYA.

Image
An haifi Abubakar Tafawa Balewa a watan Disambar shekarar 1912 a jihar Bauchi a wancan zamanin, a yankin Arewacin Najeriya. Mahaifin Balewa, Yakubu Dan Zala, dan asalin Gere ne, kuma mahaifiyarsa Fatima Inna yar Gere ce kuma asalin Fulani ce. Mahaifinsa yana aiki a gidan hakimin Lere, gundumar cikin masarautar Bauchi. Karatu Balewa ya fara karatunsa ne a makarantar Alkur’ani da ke Bauchi; lokacin da masu mulkin mallaka na kudu suka fara yunÆ™urin ilimantar da mutanen yankin Arewa, Balewa yana cikin yaran da aka tura makarantar Elementary ta Tafawa Balewa, bayan kammala karatun Alqur’ani. Daga nan ya wuce Makarantar Lardin Bauchi.  Kamar sauran mutanen zamaninsa, ya yi karatu a Kwalejin Barewa wadda a lokacin ake kira Katsina College, inda ya kasance dalibi mai lamba 145. Ahmadu Rabah, wanda daga baya aka fi sani da Ahmadu Bello, dalibi ne mai lamba 87, kuma yana da shekara biyu a sama, yayin da Abubakar Imam ke gabansa shekara guda. Kwalejin dai na da tazarar kilomita da...

NASIHA

Image
NASIHA KYAUTA-: 1. WASA idan yayi yawa yana kawo                    SHAGALA. 2. SURUTU  idan yayi yawa yana kawo                    KARYA 3. WAYEWA idan tayi yawa tana kawo                    KAUYANCHI 4. JAYAYYA idan tayi yawa tana kawo                   GABA. 5. SON DUKIYA Idan yayi yawa yana kawo.                   CHIN HARAM 6. WAYO idan yayi yawa yana kawo.                   ZALUNCHI. 7. KARFI idan yayi yawa yana kawo                   MUGUNTA. 8. ROKO idan yayi yawa yana kawo                   WULAKANCHI. 9. TUNANI idan yayi yawa yana kawo                 ...

AMFANIN KANWA A RAYUWAR DAN ADAM

Image
Amfanin kanwa a rayuwar ɗan Adam Wani nau'i na kanwa da aka samu a garin Vielsalm na ƙasar Belgium Sa'o'i 4 da suka wuce Kanwa suna ne da ake kiran rukunin ma'adanin ƙasa ko sinadarai da ke ƙunshe da sinadarin potassium, wanda ke gina jikin tsirrai. Ana iya cewa babban amfanin kanwa a fannin masa'antu shi ne haɗa takin zamani. A fannin lafiyar ɗan Adam kuma, sinadarin potassium na da muhimmanci wajen haɓaka gaɓɓai da kuma naman jikin mutum, har ma da wani ɓangare na ayyukan zuciya. Sai dai wasu masana lafiyar abinci sun ce rashin amfani ya fi amfaninta yawa game da yadda mutane ke sha da kuma amfani da ita a abinci. Ana haƙo kanwa ne a wuri mai dausayi. Ƙasashen da suka fi samar da kanwa a duniya Yadda ake haƙo kanwa a ƙasar Canada a shekarun 1970 Shafin intanet na gwamnatin ƙasar Canada ya bayyana cewa ƙasar ce ta fi kowacce haƙowa da fitar da kanwa a duniya. Canada na fitar da kashi 31 na kanwar da ake cinikayayya a duniya duk shekara ya zuwa 2020. Ƙas...