sarkakiyar soyayya part 3
……
INA ASHE GUDUN BANZA NAYI HAR GIDA ZATA BIYONI TAMIN.
Cikin sauri na juya da gudu nabar cikin garejin ko kayana ban chanja ba. Ina fita ko mashin dina ban dauka ba gudun karna tsaya dauka tazo tasa meni. Ina fita bakin titin dayake garejin namu a bakin hanya yake. Cikin sauri na tari me adaidaita sahu nace yakaini wani unguwa dake kusa da unguwarmu.
Ana saukeni a unguwar na rasa inda zanje kawai sainayi shawaran inkoma gida na bugawa wani dan garejin mu waya nace yatawo min da mashin dina gida yace to. Haryake gayamin cewa ameera
tasha kuka acikin garejin waina yaudareta.
Sauri nayi na kashe wayan na fada cikin wani botiq nasayi kaya domin cewa yanda akemin
kallon babban yaro a unguwar mu bazan iya shiga da kayan gareji ba.
Bayan nasiyi kaya na chanja saina bugawa abokin harkata usman na gayamai cewa yaufa rana ta kwa6e. Kazo da motarka ka daukeni kasan bazan iya hawa adaidaita sahu inzo gidaba dan kasan ana biki akan layinmu akwai yan mata dayawa yace to.
Minti 20 yayi yawa saiga usman yazo acikin motansa joka ya daukeni yakawo ni gida. Nake
gayamai idan nasamu nutsuwa zan basa labarin abinda ya faru dani yake ok.
ina shiga cikin gida banyiwa kowa magana ba. Kawai dakina naje na kwanta naji zuciyata tana bugawa sosai. Dukda fankan dakina akunne yake amma be hana gumi fitowa
daga sassan jikina ba. Kawai sainaji wayata tana ringi ina dubawa sainaga ameera ce naki dauka. Ta dinga bugawa bana dauka daga karshe kawai
saina kashe wayan ban kunna ba saikusan sha 11 da rabi na dare abinda yasa na kunna danna hau facebook ne ko whatsapp waiko zanrage bakin cikin dake damuna.
Kawai sainaji wasika ta shigo cikin wayata saina bude naga anyi rubutu kaman haka..
A GASKIYA KABAN KUNYA WALLAHU DAMAKAI MAKARYACI NE. MAYAUDARI. MACI AMANA. A GASKIYA HUSSAIN KA CUCI KANKA DAKAMIN KARYA. AMMAFA KASANI DUKDA HAKA INASON KA DOMIN CEWA NASAN BA LAIFINKA BANE SHARRIN SHEDAN NE KUMA BATURE YACE MISTAKE IS NOT A MISTAKE UNTIL U RFT MSTK
IS A MSKT SABODA HAKA KADAWO MUCI GABA DA SOYAYYA DOMIN CEWA INA SONKA. NAMA GODEWA ALLAH INDAKAI BA BARAWO BANE I LOVE U
ina gama karanta wannan wasikan narasa gane
awani hali nake ciki farin ciki ko bakin ciki.. A haka harnayi bacci
bayan sati 1 da faruwar wannan lamarin ina kwance acikin falon gidan mu ina kallo naga kanwata farida sai shirye shirye take wanda bansaba ganinta awannan halin ba.
Dadai na gaji da ganinta haka saina tambayeta ke Lafiya kike shirye shirye haka sai tace dani yau zatayi babbar bakuwa kawatar wacce sukayi secondary tare zatazo yau. Nace ok. Tace dani amma yaya HUSSAINI idan tazo zankawo maka ita ku gaisa dan ina yawan bata labarinka nace to
bakomai.
Tun lokacin da abinnan yafaru tsakani na da ameera bankara daga wayanta ba. Kuma akullun
saita kirani yafi a kirga.. Misalin karfe 12pm ina zaune acikin dakina sainaga kanwata aeesha tayi sallama tace dani ga kawar tawa tazo naje mugaisa nace to. Fitowa nayi domin mu gaisa ina fitowa sai idanuwana sukamin arba da ameera
“tirkashi babu daman guduwa gatanan harcikin gidanmu”
Jinayi kaman na bace alokacin da idanuwane sukayi ido hudu da ameera.
Amma ina jikina yana karkarwa nakarasa wajenta. Nayi karfin hali nayi mata sallama.
Watsomin harara tayi sannan ta bude bakinta cikin sheshshekar kuka tace dani.
N…guys kenan lalle kacika namijin duniya dama ace duk kalan yanda kake nunawa kana
sona afili ne kawai amma bekai cikin zuciya ba??
Kayi aiki da kalamanka masu dadi ka yaudare ni.
Ka cusamin kaunarka acikin zuciyata ka tafi kabarni.
Yanzu yaya kake so nayi da kaunar ka??
Shiru nayi nakusan dakika 40 kafin na budi baki dakar nace da’ita ameera tare dani babu yaudara acikin zuciyata.
Illa so da kaunar ki dayake dada karuwa kullun acikin zuciyata.
Tun randa wannan abin yafaru tsakanina dake bacci ya kauracewa idanuwa na walwala da farin ciki sun dishashe daga fuskata. Bazan iya kirga adadin yawan lokacin dayake shudemin arana ina cikin tunanin kiba. Narasa da wacce fuska zan kalle ki harna baki hakuri.
Kuma na gaya maki dalilin dayasa nayi maki haka.
Dama ace zakiji dalilin da na tabbata saikin tausayamin.
Amma yanzu yazama dole na gaya maki dalilin ko zaki daina zargin da kikemin na mayaudari
maci amanata. Aduk lokacin danaji wannan kalman tafito daga bakin ki jinake kaman na
kashe kaina dan tsabagen bakin ciki.
Ameera tace dani dama nasan cewa dolene kayi amfani da dadan kalaman ka wajen kara
yaudarata.
Nace da ita a’a babu maganan yaudara atare dani da’ace zaki saurari labarin dazan baki na tabbata dasaikin tausayamin.
Tace to gayamin labarin dahar yasa kamin karya nan take na budi baki na fara bata labarin kaman haka.
Nan take ameera tace to kaban labarin naka naji. Nace to. Kunade biye dani ko????
Zamuci gaba a part 4 gobe in allah ya kaimu a wannan shafin.
Comments
Post a Comment