IDAN KANA SON KA TSIRA A NIGERIA
IDAN KANA SON KA TSIRA A NIGERIA 👇 (1) Ka sani ba'a yin kudi da albashin Gwamnati a Nigeria, sai dai idan ka samu dama a cikin Gwamnati kayi satar dukiyar al'ummah wanda a karshe zakayi nadama marar amfani a duniya da lahira (2) Don haka tunda albashin Gwamnati ba zai wadataka ba wajen biyan bukatun kanka da na iyalanka, mafita a gareka shine ka hada da sana'a ta halal komin kashinta da kuma noma da kiwo, zasu rufa maka asiri Insha Allah (3) Ka dage kayi karatun zamani a fannin da zamani ke bukata, wato kimiyya da na'ura mai kwakwalwa da fannin kiwon lafiyar mutane da dabbobi, fannin noma da kiwo da makanikanci, ma'ana yanzu ana neman ilmin da zai sa ka koyi sana'a ne, kar ka tsaya bata lokaci wajen karanta political science (4) Ka sani cewa Masana kimiyyar zamani sunyi taro a Kasar Saudiyyah, Professor Isa Ali Pantami ya halarci taron, anyi amannar cewa nan da shekaru 15 kaso 75 cikin 100 na mutane ma'aikata a duk fadin duniya zasu...