IDAN KANA SON KA TSIRA A NIGERIA

IDAN KANA SON KA TSIRA A NIGERIA

👇
(1) Ka sani ba'a yin kudi da albashin Gwamnati a Nigeria, sai dai idan ka samu dama a cikin Gwamnati kayi satar dukiyar al'ummah wanda a karshe zakayi nadama marar amfani a duniya da lahira 

(2) Don haka tunda albashin Gwamnati ba zai wadataka ba wajen biyan bukatun kanka da na iyalanka, mafita a gareka shine ka hada da sana'a ta halal komin kashinta da kuma noma da kiwo, zasu rufa maka asiri Insha Allah

(3) Ka dage kayi karatun zamani a fannin da zamani ke bukata, wato kimiyya da na'ura mai kwakwalwa da fannin kiwon lafiyar mutane da dabbobi, fannin noma da kiwo da makanikanci, ma'ana yanzu ana neman ilmin da zai sa ka koyi sana'a ne, kar ka tsaya bata lokaci wajen karanta political science

(4) Ka sani cewa Masana kimiyyar zamani sunyi taro a Kasar Saudiyyah, Professor Isa Ali Pantami ya halarci taron, anyi amannar cewa nan da shekaru 15 kaso 75 cikin 100 na mutane ma'aikata a duk fadin duniya zasu rasa guraben ayyukansu a masana'antun Gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu, za'a maye gurbinsu da Artificial Intelligence da Robotics domin a rage yawan kudin da ake kashewa mutane ma'aikata

(5) Dan uwana talakan Arewa ka rage yawan bacci cikin dare, duk wanda kaga yayi arziki ko ya tara ilmi mai amfani sai da ya hana idonsa bacci, dukkan sirri na daukakar rayuwa da arziki yana cikin Qiyamullaili 

(6) Ka yi hankali da mutane, ka zama mai tsananin rike sirri har sai kaji tamkar kai kanka baka yadda da kanka ba balle wani makusanci, yanzu muna lokaci ne na tsananin cin amana

(7) Yanzu an dena kiwon dabbobi an koma kiwon mutane, ka zama mai yawan canza hanya idan zaka tafi wani guri ko gari, duk lokacin da kazo hawa abin hawanka ka leka kasan tayun motarka ko babur dinka, idan kaga alamar an tona rami to ka duba da kyau saboda miyagu suna da hanyoyin cutarwa da yawa

(8) Wani Malamina da yake bani horo akan Cyber Forensic yace min ka zama mai yawan gani da sauraren mutane, amma ka zama mai taka tsantsan wajen magana dasu kai tsaye, idan zakayi maganar ka fadi kalmomi kadan ka rufe bakinka, kuma a duk inda alaka ta hadaka da wani ka nuna masa kai wawa ne, musamman idan shi din ya nuna maka mai wayo ne, yace min zaka samu ilmin rayuwa mai dumbin yawa

(9) Dan uwa duk runtsi duk wuya kar ka yadda ka zama dan iska, babu wata riba da ake samu a zama dan iska, kar ka fara shaye-shaye da neman matan banza, suna gadar da talauci, ka kulla abota da wadanda suka girmeka da kuma wadanda suka fika ilmin addini da zamani, ka dena nuna kanka koda Allah ya baka wata baiwa

(10) Kar ka yadda da boka ko Malamin tsubbu makaryatane mayaudara kuma 'yan damfara ne, ka nema a gurin Allah Shi Kadai (SWT)

(11) Duk wata harka da za'ayi wanda ya shafi cutarwa ko kwace hakkin wani kayi gaggawan tsame kanka daga ciki, imba haka ba makiyanksa zasuyi nasara a kan ka

(12) Idan ka shiga harkan gwagwarmaya to sai ka rike gaskiya da amana gam, idan ba haka ba  to ba zakayi lasting ba, makiya zasu kaika kasa

 (13) Kar kayi wasa da addu'ah, addu'ah yafi Makamin Nukiliya karfi da tasiri wajen karya lagon abokan gaba da mummunan kaddara ta rayuwa

Allah Ya sa mu wanye lafiya

Copied

Comments

Popular posts from this blog

TSAMMANIN DAKE ZUCIYOYIN MUTANE GAME DA JIMA'I A ZAMANIN YAU.

NASIHA