Sarkakiyar soyayya part 1
sararin samaniya dauke yake da gajimare hakan ne yasanya garin yayi sanyi me dadi gami da iska me busowa a hankali.
Garin cike yake da jama’a ko ina duk inda ka Waiga ba abinda zaka gani illah kawunan mutuna
da muryoyinsu ba komai bane ya haddasa haka illah ana gobe sallah burin kowa yaje kasuwa yayi siyayyan sallah .
tashi wata daga garejin gyaran mota kenan bayan na wanke jikina nasa kayan gida harna nufi wajen mashin dina sainaji ana kirana hussaini hussaini cikin sauri na juyo domin cewa muryan ogana naji….
Gani oga abinda nace kenan lokacin dana karasa Wajensa. Yace dani hussaini ga key din motata kaje kashawo min mai kadawo nace to amma ba’ason raina ba saboda akwai wani wasa da akeyi yau inaso naje na gani.
Cikin sauri naje inda ogan mu yake aje motan sa na tuka na fito dashi waje ina fitowa sainaji ana hussain ina juyawa sainaga yarinyar datake kawo mana abincine dama naci abinci ban biyata ba. Kawai na daga mata hannu alamun ina zuwa.
A hankali nake tuka motan ba wani gudun kirki nakeyi ba saboda garin akwai cinkoso dayawa.
Tafiya nake a hankali nakunna wakan nura m inuwa [abin sona] Tun daga nesa idanuwata suka hangomin wata kyakkyawar budurwa ajin farko acikin yan mata. Kyawun nata yawuci hankalin me kwantace.
Ina matsowa kusa sainaga cewa ta tsaya agefen titi ajikin wata mota da alama cewa motan nata ya bacine.
Harna wuceta sainayi ribas na dawo nayi fakin din motata a gefe.
Ina zuwa wajen tashin farko nace da ita AMINCIN ALLAH YA TABBATA GA YAN MATA KYAWAWA KAMAN YANDA KIKE KYAKKYAWA.
Fuska tayi ko daga ido batayi ta kalle niba balle tasan da’akwai mutum a wajen. Nakara da cewa.
Nasan cewa dama zaiyi wuya ki amsa sallamata saboda ba kimarki bane a matsayinki na babbar mace me aji da kima ki tsaya kina kula na miji akan titi?? Nikaina nasan nayi kuskure amma kisani cewa bakomai bane yasa natsaya illa naga alaman kaman kina bukatan taimako. Amma saide wani bari na zuciyata ya gayamin cewa ba lalle bane ki amince da taimakon dazan maki inda inada yakinin cewa ke daban kike a cikin yan mata.
Ina zuwa daidainan a maganata sainayi shiru. Saida takai kusan 30 secon kafin nan ta juyo ta watsamin wani kallo wanda yasa naji jikina ya mutu. Ta budi bakinta tace taya akayi kasan ina bukatan taimako?
Tsabagen tsananin zakin muryata saida yasa na manta a inda nake. Ta kara watsomin tambayan a karo na 2. kafin na budi maki dakar nace da ita. Naga kaman motanki ta samu matsala kina bukatan makaniki tace eh. Nace idan zaki amince
yanzu na kira maki makanikina yazo ya gyara maki tace to a hankali. Nace bari na dauko wayata acikin mota ina shiga
cikin mota na dauko wayata na bugawa abokina waya me suna salisu shima makanike ne Yana
gyaran motane . Kuma abokinane sosai. Kawai saina gayamai wasu magana. Fitowa nayi nasameta nace na kira maki makanikin yana zuwa ba’afi minti goma 15 ba saiga salisu yazo yana zuwa nace mai wannan motan zaka duba mana taki tashi yace to.
cikin yan mintina harya gama gyaran motan. Yatashi motan. Ta budi baki tace nawa za’a
biyaka yace ai oga yabiya tace waye oga ya nunani. Hmm tamin murmushi me taushi tace
nagode. Nace bakomai sainace dan allah wani taimako nake nema tace tame. Nace kozan iya samun phone no Naki da
address kawai saitayi murmushi ta mikomin wani
kati na’amsa nace amma saide bansan sunan gimbiyan ba?? Tace sunana AMEERA nace nice name nikuma sunana hussaini amma zaki’iya kirana N.guys
Ade haka muka rabu da’ita amma da alama ina ganin nasamu shiga. Washe gari da sassafe dayake ranan sallah ne bayan mundawo daga idi. Kawai saina bugawa ameera waya mundade muna hira daga karshe nake tambayanta yaushe zanzo gidansu. Tace duk randa kashirya. Nace zanzo da yamma.
Da misalin karfe 4pm nashirya nayi niyar tafiya gidansu amira.
Saide amsamu matsala naje wajen yayana yaban motansa nafita dashi shima yace fita zaiyi.
Kawai saina karasa gidanmu nayi sa’an babana yana gida cikin sauri na garzaya cikin dakinsa na dauko mukullin motansa ba tare dana tambaye
saba.
gudu nakeyi sosai acikin motan na nufi hanyar gidansu ameera bansha wuya ba wajen gane gidansu saina tsaya akofan gidansu nayi mata waya nace ganinan a kofan gidansu tace inshigo horn kawai nayi me gadi ya budemin gat nashiga naje na aje motata a inda ake aje motoci dannaga motoci
dayawa awajen fitowata daga motan keda wuya idanuwana
sukamin arba da wasu manyan abubuwa wanda yasa nayi dana sanin shigowata gidansu
Hankalina yayi balakin tashi sakamakon abinda idanuwana suka ganemin acikin gidan..wayyo aallah na.
……..
Zamuci gaba a part 2 gobe in allah ya kaimu a wannan shafin
Ku kasance tare damu a kullum masoya.
Comments
Post a Comment