sarkakiyar soyayya part 5
…….
Yacemin waye babanka? Wani makami babanka ya taba rikewa a 9ja sanata ko dan majalisa gidajen sa nawa??
Hmmm nan take naji kirjina yana dukakan uku uku nace dashi babana shine muhammad mahmus kuma shi bama dan siyasa bane dan kasuwa ne.
Yakara watsamin wata tambaya kai menene aikinka a’ina kayi makaranta??
Kuma kanada million 100 a account nace ni ina aiki a PAKI MOTORS nayi karatu na a 9ja
kuma sannan ma ko gamawa banyi ba ,bayan kamar daqiqa 10 na had’iyi yawu sannan na lumshe ido adede lokacin da
muka had’a ido da ameena, adede lokacin aga hawaye na xuba daga dara=daran idanunta ixuwa lallausan kumatunta me kyawun gani ,kawai setai qarpin hali ta d’agamin kai alamun naci gaba da masa bayani,seta kama hanya ta fita.sannan nai
masa magana cikin tattausar murya nace ni gaskiya ko dubu dari 3 bandashi balle million 100 sai baban nata yace dani
gaskiya bazan baka auren yata ba. Kuma ina me maka warning da cewa karka kara zuwajenta zance inkuma nakara ganinka
zakaga abinda zaibiyo baya. Ihu gami da kuka mukaji ankwala hakanne yasa mukayi saurin juyowa ashe amina tana bayan mu tanajin mu.ni nayi xaton fita tayi, Ta dinga cewa wallahi baba ni’ina sonsa. Cikin sauri na juya na nufi hanyar fita daga gidan,ina tapiya ina waige jinake kamar xaisa a capkeni dan nasan a yadda naga alamunsa yana da kud’in daxe iya sawa igiya tayi rara akai na
saida nakai wata 2 bankara sa ameena acikin idona ba. Wata rana na shiga shop @ she–she domin nayi siyayya. Kwatsam saina ganta awajen a gaskiya
dukta rame tayi baki bakaman daba ina ganinta cikin sauri nayi niyar fitowa dankar muhadu ashe ta ganni. Saita biyoni. Ina fitowa tasha gabana tace dani
gaskiyane hussaini dama son da kakemin abakine kawai baikai har cikin zuciya ba kaida kake ikirarin cewa ko duk duniya zasu taru akanka basu isa su rabani dakai ba?? Amma tunda abinnan yafaru tsakaninka da
mahaifina ka kauracemin?? Mezai hana ka daukeni mubar garinnan muje wani gari muyi aure?? Jin d’and’anon gishiri ne a bakina ya tabbatarmin cewa hawaye ne ke kwarara daga idanuna xuwa fuska ta
kafin wani lokaci idona yakad’a yayi ja jawur. Na dubeta cikin tausayawa gamida magana cikin sassanyar murya me dauke da sinadarin cire damuwa da qunci gamida
kawo yalwataccen farin ciki da annashuwa me kuma kawar da dukkan wata damuwa da samar da walwalar xuciya,cikin rawar
murya Nace da ita ameena a gaskiya ina sonki fiye da yanda
nakeson kaina ina sonki fiye da tunanin me tunani domin kuwa soyayyarki dabance acikin rayuwata ameena na tabbata kin kapamin tarihin da baxan manta dashi ba danko kin samu nasarar mallake xuciya
ta,kuma yanxu haka xuciyata bata tare dani tana gurinki,kina tarbiyyantar da ita soyayya tare da tare da ilimantar da ita soyayya ta gaskiya,hakan tasa akoda yaushe nake d’abi antuwa da kyawawan halayenki har mutane suke mamakin yadda na canja a d’an qanqanen lokaci……..kawai ban gamaba na pashe da kuka itama ta maramun baya mukaita kuka tare aka rasa me rarrashin
wani,kawaisetai qarpin hali tasa kyawawan hannayenta masu d’auke da xobuna 2 na axurpa da tagulla,tapara sharemin
hawayena,aiko kamar anyi ruwa an d’auke nayi tsit,tasa hannu a jakarta ta dakko bandir na en dari biyar=biyar tabani na6ata
rai nace ba wannan ne damuwata ba kece…. amma saide babanki ya rabani dake.
Yanzu kawai hakuri yakamata muyi. Ina gama fada mata wannan maganan nayi tafiyata kawai ta sakamin kud’innan a
kwandon mashin d’ina itama ta tapi.raina yaqara 6aci. Ina zuwa gida ta bugamin waya tacemin
komai tsanani komai wuya saita aureni.
ina zuwa daidainan gun a labari na na kalli ameera nace da’ita kinji labarin dayasa nayi maki karya kuma ada na dauka kudi shine soyayya. Ameera tace dani a gaskiya kayi kuskure
daka dauki haka amma yanzu nagane cewa kudi bashi bane so ni hussaini na juya na kalli ameera na bata hakuri
tace bakomai munci gaba da soyayya da ameera kaman da cikin gaskiya da rikon amana da kaunan juna alhamdulillah.
nanne karshen labarina na sarkakiyar soyayya. Ina mika gaisuwa ga dukkan masoya labarai na. SARKAKIYAR SOYAYYA part 5
KARSHE
Karshen labarin KENAN.
Mu hadu daku masoya domin nishadantarwa alakhairin.
Comments
Post a Comment