TARIHIN HAUSAWA DA AL'ADUNSU.

Hausawa al'umma ce dake zaune a arewa maso yammacin tarayyar Nijeriya da kudu maso yammacin jamhuriyyar Nijar. Al'umma ce mai ɗimbin yawa, sun bazu a cikin ƙasashen Afirka da ƙasashen Larabawa kuma a al'adance masu matukar hazaƙane, aƙalla akwai sama da mutane miliyan hamsin wadanda harshen Hausa shi ne asalin yarensu. A tarihi ƙabilar Hausawa na tattare a salasalar birane watau alqarya. Hausawa dai sun sami kafa daularsu ne tun daga shekarun 1300's, sa'adda suka sami nasarori da dauloli kamar su daular Mali, Songhai, Borno da kuma Fulani, a karni na 19 Hausawa suna amfani da Doki ne domin yin sifiri da balaguro.[1] Mutane kimanin sama da miliyan 50 ne ke magana da yaren hausa a Najeriya, Nijar, Arewacin Gana da kuma wasu al’umma daga yankin Kaolack a senigal har zuwa khartum dake ƙasar sudan, Asalin inda zuciyar hausawa take shine garin Kano, Katsina da Sokoto.[2] Asalin hausawa maguzawa ne, a ƙarƙashin mulkin sarakunan Haɓe, wanda suke yin bori da tsubbace-tsubbace, zuwan Shehu Usman Ɗan Fodio ne yasa ya jadddada addinin ƙasar hausa, ta hanyar yaƙar maguzawa da sarakuannasu na haɓe a Gobir, Zazzau da wasu yankunan ƙasar hausa. Wanda wannan jihadin ne yasa Usman Ɗan Fodio ya kafa Daular Khalifanci na Hausa Fulani a ƙasar hausa, kuma da yawan hausawa suka karba musulunci a ƙasar hausa. Hakan yasa masarautun ƙasar hausa sun kasance a ƙungiyar Tuta ɗaya na Usman Ɗan Fodio. Hausawa suna kiran al’adunsu da al’adan gargajiya, wacce sukeyi duk shekara, ko a talabijin ko Bidiyo, ko kuma aikace cikin al’amuran yau da kullum. Na daga cikin rubutun hausawa, suna yin rubutu ne asali da Ajami, rubutu ne da haruffan larabci amman a luggar hausa, kuma suna rubutawa ne a fallen takarda.

Comments

Popular posts from this blog

TSAMMANIN DAKE ZUCIYOYIN MUTANE GAME DA JIMA'I A ZAMANIN YAU.

NASIHA