TAKAITACCEN BAYANI KAN MACE!
Mace Halitta ce mai tsaurin rai, Amma hawayenta a kusa yake, tana da saurin kamuwa da so. Sai dai bata iya kiyayyaba🥰
Azahiri tana nuna karfi da juriya, Amma can cikin zuci mai rauni ce, in kana hira da ita kan abinda ke qona mata rai, idaniyarta nada saurin kuka.😢
A soyayya mace tafi kowa ikhlasi(In har ta soka da gaskia) zuciyarta bata iya daukan wani bayan kai, kaji tsoron macen da ke nuna tana son ka da gaskia Amma bata dai na kula sauran samarinta ba, Zuciyar mace na son kalmomi masu dadi, Amma sun tsani karya. 🥰
Suna iya bada soyyaya Ko sunsan baxasu samu kwatankwacinta ba😊
Mace tana da karancin bayyana soyayya da kalmomi, Amma basa iya boyeta a Aikace
Girman kan mace na tasiri har akaran kanta, wani lokutan kin Amsa kiraka ko kin Nemanka duk acikin wannan jiji da kai yake (ba rashin soyayya bane)😊
Mace bata so ka mata Alkhairi sannan katuna mata Dan tana ganin hakan (Gorine).💔
A karshe komai kayiwa mace xata iya yafema, Amma banda yaudara.😢
Zuciyar mace tafi Glass hatsari, Sabida haka ka kiyaye karyata zai iya daukar ka tsawon Rayuwa a kokarin hadata, (Bayan ta fashe) kuma baxata taba dawowa yadda take ba.🙏🙃
Ya Allah gamu gareka kahadamu da masu sanmu ameen.
Comments
Post a Comment