Kalaman soyayya 💕💕
Yarda da amincewarki gareni, sune zasu
tabbatar da soyayyarki tagaskiya a gareni!
Farin ciki baya dorewa a rayuwa sai tare da
bakin ciki, dan haka kowane hali nike bazan ta6a
mantawa dake ba masoyiyata!
Nakan raba dare ina mai roqon Allah don
neman biyan buqata, ko kinsan kece abu na farko
da nike roqo samu!
Yanayin sanyi kan sa mutum ya takura, tare
da lullu6a da qaton mayafi amma ni duk sanyin da
ake idan na tunaki sai naji tamkar yanayin zafi!
Kamar yadda kowacce bishiya kanyi rassa a
sama, kuma tayi saiwa a qasa, haka sonki ya
mamaye dukkan jikina, idan na kalleki sai nayi
farin ciki, idan naji tattausan muryarki, sai nishadi
da walwala tare da annashuwa gami da farin ciki
su mamaye zuciyata!
Abun da na ke ji a dangane da ke gaskiya ne
kema na san kin san da haka cewa ina son ki, a
duk lokacin da kika bar ni ba zan iya motsawa ko
da nan da can ba, wannan shi ne abun da zai
faru da ni a duk lokacin da na rasa ki.
SO tamkar wata sarkar zinari ce da ta d’aure
zuciyoyin mu a waje guda, a dukkan lokacin da
kika tsinka waccan sarka tofa ki tabbatar da
cewa tamkar kin kore farin ciki ne daga cikin
zuciya ta.
All my life I have searched but never found a girlfriend who is so perfect for me. With you I do not need to worry about the future ♥Assalamu alaikum sanyi idaniyata, dafatan ban shigo duniyar ki ba a matsayin bawa da zai bautu a kangin soyayya.
da fatan ni ne zan zamo YAREEMA da zai gudanar da mulki a cikin kayatacciyar fada a duniyar soyayyar
Ina rokon Ubangiji da ya bani me.
Comments
Post a Comment