sarkakiyar soyayya part 2

……..
bakomai nagani ba illa wasu manyan karnika wanda nasan cewa koya nayi motsi zasu iyi cinye ne domin cewa guda 1 daga cikinsu yakai girman zaki.
Nan take jikina yafara tsuma..
Ahankali nabi na fada cikin motata kafinnan na buga mata waya nace na shigo cikin gidanku amma naga karnika kizo mutafi tare ciki tace to. Ba’afi binti 3 dayin wayan ba na hangota tayi wani shegen shiga tun kafin takaraso inda nake tuni nazama kankara.
Tazo sai magana takemin amma banjima saboda nayi nisa acikin wata sabuwar duniya saida ta dafa kafada ta kafin nayi dogon numfashi nadawo cikin hayyacina. Tace dani lafiya Hussain tunanin me kakeyi. Nace da’ita babu komai. Ahaka muka karasa da ita cikin gidansu zuwa falon saukan baki shigana cikin falon keda wuya nafara kauyanci saboda ma alokacin dana taka kafet din falon saida nayi kara na dauka zan nutse kasa ne. Ashe laushin kafet dinne. Tace dani lafiya kayi kara nace nadan fame targadena ne. Tace sannu. Nace yauwa.
mundade muna hira da’ita kafin mukayi sallama muka rabu amma ba’ason ranta ba.
nadawo gida cikin farin ciki da annashuwa kasancewar nasamu shiga sosai wajen gimbiya ameera. Ada nayi tunanin cewa zansha wuya kafin ta amince da soyayya ta.
Saikuma gashi bansha wuya ba.
Ina shigowa harabar cikin gidan mu nayi fakin din mota. Na wuce direct dakina domin na huta. Ina shiga dakina naji handset dina yayi kara alamun an turo wasika cikin sauri na bude wasikan sainaga anyi rubutu kaman haka.
ASSALAMA ALAIKUM YAKAI SAHIBINA RABIN RAINA MIJINA NA GOBE SONKA YAYI GIRMA ACIKIN ZUCIYATA WANDA BANSAN IYA KACINSA
BA DA’ACE ZAKA ZAMA S NIKUMA NAZAMA O DA MUNHADA WATA KALMA ME SUNA [SO] INA SONKA KAMAN YANDA NAKE SON KAINA DAFATAN KA’ISA GIDA LAFIYA
ina kammala karanta wannan wasikan nayi murmushi. Kafin nima na mayar mata da replay
kaman haka. SARAUNIYAR ZUCIYATA. DUK LOKACIN DANA RUFE IDO KE NAKE GANI. HAKANAN IDAN NA BUDE YAUSHE ZAN DAINA SONKI KUWA ACIKIN ZUCIYATA? BABU MAI IYA CE GA RANAR. DON HAKA KENAN
SONKI YANA ZUCIYATA HAR ABADA.
DA’ACE ZAKI ZAMA FUKAFUKIN DAMA NIKUMA NA ZAMA NA HAGU DOMIN MUTARU MUTADA TSUNTSUN SOYAYYA. Ina zuwa daidainan a wasikata saina tura mata.
ahaka muka kasance da ameera muna soyayya me zafi cikin kwanciyar hankali da kaunar juna.
Saide kash ta waje daya na kwafsa nayi mata karya dayawa.
Kuma tunda nake bantaba zuwa da mota kala 1 sau 2 wajenta ba. Kuma bana zuwa da motan kasa da miliyan 3 sai sama da haka kasancewar yayana mota yake siyarwa nikuma makanike ne.
Wata ranan juma’a da misalin karfe 5pm na shirya na dauki mota kirar [bmw x5] awannan lokacin kalan motan duka basufi guda 5 ba a 9ja. Naje wajen ameera dashi mundade muna hira daga karshe nake gaya mata insha allahu zanje abuja gobe amma ranan lahadi zandawo tace allah yakiyaye hanya dan allah banda kalle kallen yan mata kawai sainayi dariya nace.
Ke kina tunani cewa harda akwai wata ya mace dazan kalla fadin duniya bayan inada sarauniyar yan mata. Tayi murmushi me taushi agareni wanda aduk lokacin datayi murmushin hankalina kwanciya yakeyi gami da kara sonta acikin zuciyata. [ashe karya nake mata akan zanje abuja]
ina gareji da misalin karfe 2pm bayan na idar da sallah azahar naji wayata tayi ringi ina dauka naga ai ameera ce. mundan taba hira kadan harnake gaya mata ayanzu haka na sauka a garin abuja lafiya. Tace hmm nagodewa allah. Sai mukayi sallama.
Banfi minti ashirin ba da kammala wayan naji ogana yana kirana HUSSAINI HUSSAINI nace na’am oga yace kadakata da aikin da kakeyi kaje gacan wata mota brama kayi mata service nace to.
Ina zuwa na kunce bakin man motan da filta da kuma nosin. Naje wajen ogana nace oga kaban kudi nace nasiyi bakin mai da filta da injector cliner domin awanke nosin yacemin kaje kasan bishiya akai yan mata awajen ka karbi kudin nace to.
Ina zuwa batare dana hankara ba nace hajiya kiban kudi nasayo kayan gyara budurwar tana juyowa sainaga ai ameera ce. WAYYO ALLAH
Tana kallona ta dafe kirji tace hussy nanne abujan? Dama kai mayaudari ne.
A haba ina kawai saina ruga da gudu nayi wajen gareji.
Cikin sauri na juya da gudu nabar cikin garejin ko kayana ban chanja ba. Ina fita ko mashin dina ban dauka ba gudun karna tsaya dauka tazo tasa meni.
Ina fita bakin titin….
yaya muci gaba koko sai zuwa gobe in allah ya kaima?
Zamuci gaba a part 3 gobe in allah ya kaimu a wannan shafin. Allah ya kaimu gobe kusha labari.

Comments

Popular posts from this blog

TSAMMANIN DAKE ZUCIYOYIN MUTANE GAME DA JIMA'I A ZAMANIN YAU.

NASIHA