AMFANIN ALBASA 13
![Image](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgSkMxV0PBjeBaq_omjf_pIfJ1ilQakVwxyPOFZYXzG6bhqWRr93qVh2rsnlgFGqHKgd1GS3hVG5fM7JaXhGB2peRXIXa59z6JGuynTlk3ZWVXs9gNxcSkcLrtW4c_1VqT3l0yIIdnGDUN3/s1600/1660558568218646-0.png)
Hakika albasa na da tsohon tarihi duba da yadda al'umma ke amfani da ita a harkokin abincinsu da kuma magani. Masana sun yi ittifakin cewa albasa na da wasu muhimmman sanadarai da ke taimaka wa wajen gina jikin dan-adam, baya ga haka sanadaran da albasa ke kunshe da su na da tasiri kan wasu cututtukan jiki. Shekaru da yawa da su ka shude, al'ummomin Duniya daban-daban ke amfani da albasa don magance cututtukan da ke damun su, kamar ciwon sanyin kashi, mura, ciwon makogoro da gabobi da sauran su. Ganin yadda albasa ke da amfani ga lafiyar dan-adam mu ka dacewar yin bincike don zakulowa ma'abota wannan shafi, fa'idojin albasa, kuma mun yi wannan makala lakabi da "Amfanin albasa ga lafiyar Bil-adama. A sha karatu lafiya. 1. Maganin Tari, Mura Ko Ciwon Makogoro. Daga cikin amfanin albasa ga dan-adam akwai maganin sanyi, mura ko ciwon makogoro. Duk wanda ke fama da daya ko duk ciwon da muka zana a sama, musamman wanda ke fama da tari ko mura mai tsanani, ya ...