ALAMOMIN SHEDANIN SAURAYI..'Yan mata da dama suna shiga cikintarkon shedanun samari suyaudaresu suyi ta zina da su datunanin zasu auresu saboda sashinsanin wasu taku na ma yaudaranmaza..Ga wasu daga cikin alamun da zaki yisauri da saukin fahimtar saurayin konamijin da yanzu haka kike soyayyadashi ba aurenki yakeson yi ba zinakawai yake son yi dake.1: Zaki ga cewa bai yabon halayenkiko dabi'unki masu kyau kullummaganan halittun jikinki yafimagana maimakon wasu halayenki.2: Bazai miki maganan aure ba kumaidan kin masa bai daukan zancen damahimmanci.3: Yana gudun 'yan uwanki danashisu ganki. Don haka da wuyayagabatar dake a wajen wasu nakusa dake kuma zai rikakaucemiki idan kika bukaci yagawasu naki nan ma zai rika zullewa.4: Mafiyawan lokaci yafison kiziyarceshi maimakon shi ya rikazuwa wajenda kike.5: Yana son gayyatarki wurarenshakatawa da holewa maimakonwajen da zaki samu karuwa naaddini ko na wani ilimin zamani.6: Wasu alamun shine idan kikayiwani kuskure baya iya fitowa a fili yanuna miki saboda babu son gaskiyaa zuciyarsa kada ranki ya baci.7: A duk lokacin da kuka kadaitaburinsa shine ya tabaki ko ya jawokia jikinsa.8: Sakonninsa na waya zantukanbatsa da yabon halittarki sunfi yawamaimakon wasu maganganu da zaimiki masu mahimmanci.9: Duk hiran da zaku yi da wuya yarika zuwa miki da zantunka da zaiamfani rayuwanki. Ko hira yadda zaitaimaki rayuwanki.10: Bai damuwa da kokarin saninki,tarihin ki dana zuri'arku. Ko saninabubuwan da kike burin yi ko zamaba...Wadannan sune wasu daga cikinalamun da zaki iya fahimtar saurayinnamiji mai sha'awan zina dake baaure ba.

ALAMOMIN SHEDANIN SAURAYI.
.
'Yan mata da dama suna shiga cikin
tarkon shedanun samari su
yaudaresu suyi ta zina da su da
tunanin zasu auresu saboda sashin
sanin wasu taku na ma yaudaran
maza.
.
Ga wasu daga cikin alamun da zaki yi
sauri da saukin fahimtar saurayin ko
namijin da yanzu haka kike soyayya
dashi ba aurenki yakeson yi ba zina
kawai yake son yi dake.
1: Zaki ga cewa bai yabon halayenki
ko dabi'unki masu kyau kullum
maganan halittun jikinki yafi
magana maimakon wasu halayenki.
2: Bazai miki maganan aure ba kuma
idan kin masa bai daukan zancen da
mahimmanci.
3: Yana gudun 'yan uwanki danashi
su ganki. Don haka da wuya
yagabatar dake a wajen wasu na
kusa dake kuma zai rika
kaucemiki idan kika bukaci yaga
wasu naki nan ma zai rika zullewa.
4: Mafiyawan lokaci yafison ki
ziyarceshi maimakon shi ya rika
zuwa wajenda kike.
5: Yana son gayyatarki wuraren
shakatawa da holewa maimakon
wajen da zaki samu karuwa na
addini ko na wani ilimin zamani.
6: Wasu alamun shine idan kikayi
wani kuskure baya iya fitowa a fili ya
nuna miki saboda babu son gaskiya
a zuciyarsa kada ranki ya baci.
7: A duk lokacin da kuka kadaita
burinsa shine ya tabaki ko ya jawoki
a jikinsa.
8: Sakonninsa na waya zantukan
batsa da yabon halittarki sunfi yawa
maimakon wasu maganganu da zai
miki masu mahimmanci.
9: Duk hiran da zaku yi da wuya ya
rika zuwa miki da zantunka da zai
amfani rayuwanki. Ko hira yadda zai
taimaki rayuwanki.
10: Bai damuwa da kokarin saninki,
tarihin ki dana zuri'arku. Ko sanin
abubuwan da kike burin yi ko zama
ba.
.

Wadannan sune wasu daga cikin
alamun da zaki iya fahimtar saurayin
namiji mai sha'awan zina dake ba
aure ba.
Da fatan idanuwaku zasu bude ku iya
fahimtar masu sonku na gaskiya.

Comments

Popular posts from this blog

TSAMMANIN DAKE ZUCIYOYIN MUTANE GAME DA JIMA'I A ZAMANIN YAU.

NASIHA