Kalaman soyayya 💕💕
![Image](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEicx7sxZRu6qHVt0ENYEwYZg67JpaYwU-CAUnI9prU9vo0qX7gJwN9VbzzIyFZykrEE7Z_n0YCeFtC1lQ8EWOeLCSCzahjHUV75gFLrTLmvKrHX2BKDzbPmebaMhMrFpbwZbD21N8wPoT08/s1600/1653244021949064-0.png)
Yarda da amincewarki gareni, sune zasu tabbatar da soyayyarki tagaskiya a gareni! Farin ciki baya dorewa a rayuwa sai tare da bakin ciki, dan haka kowane hali nike bazan ta6a mantawa dake ba masoyiyata! Nakan raba dare ina mai roqon Allah don neman biyan buqata, ko kinsan kece abu na farko da nike roqo samu! Yanayin sanyi kan sa mutum ya takura, tare da lullu6a da qaton mayafi amma ni duk sanyin da ake idan na tunaki sai naji tamkar yanayin zafi! Kamar yadda kowacce bishiya kanyi rassa a sama, kuma tayi saiwa a qasa, haka sonki ya mamaye dukkan jikina, idan na kalleki sai nayi farin ciki, idan naji tattausan muryarki, sai nishadi da walwala tare da annashuwa gami da farin ciki su mamaye zuciyata! Abun da na ke ji a dangane da ke gaskiya ne kema na san kin san da haka cewa ina son ki, a duk lokacin da kika bar ni ba zan iya motsawa ko da nan da can ba, wannan shi ne abun da zai faru da ni a duk lokacin da na rasa ki. SO tamkar wata sarkar zinari ce da ta d’aure zuciyoyin mu ...